Isa ga babban shafi
Masar

Adadin magoya bayan Morsi da aka kashe a Masar na ci gaba da karuwa

Rahotanni daga kasar Masar na nuna cewa adadin magoya bayan hambararren shugaban kasar Masar, Muhammad Morsi da suka rasa rayukansu wanda aksarin ‘yan jam’iyar ‘Yan uwa Musulmi ne na ci gaba da karuwa yayin da ake zargin jami’an tsaron kasar da aiwatar da kashe kashen.

Ana bawa wani mai goyon bayan hambararren shugaban kasar Masar Mohammed Morsi taimako a asibiti
Ana bawa wani mai goyon bayan hambararren shugaban kasar Masar Mohammed Morsi taimako a asibiti REUTERS/Suhaib Salem
Talla

Masu ba da agajin gaggawa a kasar ta Masar sun sanar da cewa adadin a lokacin hada wannan rahoto ya kai mutane 42 yayin da wasu 322 suka samu raunuka daban daban.

“Adadin wadanda aka kashe ya kai 42, sannan wasu 322 sun samu raunuka.” Inji Ahmed al Anasri, wani mataimakin shugaban masu ba da agajin gaggawa a Masar.

Jam’iyar ‘Yan uwa musulmi wacce a ciki Morsi ya yi takara wacce kuma ke jagorantar zanga zangar hambarar da Morsi ta bayyana cewa mutane 35 daga cikin wadanda aka kashe mambobin ta ne.

Tun a karshen makon da ya gabata ne jam’iyar ta bayyana cewa ba za su ja da baya ba wajen gudanar da bore a kasar har sai sojin kasar da suka hambarar da Morsi a ranar Larabar da ta gabata sun mayar da shi kan karagar mulki.

Jam’iyar ta zargi soji da kuma ‘yan sandan kasar wajen kashe mata mabobin inda a safiyar yau Litinin ta yi wani sabon kira na a yi bore a daukacin kasar.

Wasu shaidun gani da ido ciki har da mambobin jam’iyar sun wanke jami’an tsaro daga wannan zargi inda suka ce ‘yan adawa ne suka kai hare haren da ya yi sanadiyar mutuwar mutanen.

Rahotanni har ila yau sun ce dakarun kasar sun rufe hedkwatan jam’iyar ta ‘Yan uwa musulmi bayan an yi zargin samun wasu makamai a ofishinta da suka da sinadaran hada wuta.

Tuni dai aka fara Allah da wannan kashe kashe da aka yi a kasar ta Masar inda shugaban ‘yan adawan kasar, Mohammed Elbaradei ya yi Allah wadai da kashe kashen ya kuma yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa a gurguje.

“Ba a magance tashin hankali da tashin hankali, ya kuma kamata a yi Allah wadai da hakan.” Inji Elbaradei wanda ya bayyana ra'ayin nasa a shafinsa na Twitter.

Itama kasar Turkiya ta bayyana ra’ayinta game da kisan inda ta yi Allah wadai da hakan.

“Muna Allah wadai da kakkausan suka akan wannan kashe kashe da aka yi, wanda ya sabawa ‘yancin dan adam.” Inji Ministan harkokin wajen kasar, Ahmet Davutoglu.

Tun a ranar juma’a, shugaban kasar, Recep Tayyip Erdogan ma ya yi Allah wadai da hambaren gwamnatin Morsi inda y ace hakan ya sabawa ka’idojin demokradiya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.