Isa ga babban shafi
Isra'ila-Felesdinu

Isra’ila da Falasdinawa za su koma teburin tattaunawa- Kerry

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce ya samu nasarar shawo kan hukumomin kasar Isra’ila da na Falasdinu domin sake komawa kan teburin tattaunawa bayan share kusan shekaru uku da rugujewar tattauwar. Kerry ya fadi haka ne a Jordan bayan ya gana da bangarorin biyu.

John Kerry Sakataren harakokin wajen Amurka a lokacin da ya ke ganawa da Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas a Fadarsa da ke Ramallah
John Kerry Sakataren harakokin wajen Amurka a lokacin da ya ke ganawa da Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas a Fadarsa da ke Ramallah Reuters
Talla

Kerry wanda ya kawo karshe ziyara ta 6 da ya kai a yankin gabas ta tsakiya daga lokacin da aka nada shi kan wannan mukami, ya ce dukkanin bangarorin sun amince da sake farfado da wannan tattaunawa, kuma nan ba da jimawa ba ne zai sake ganawa da jagoran tawagar Falasdinu, Saeb Erakat da kuma ministan shari’a ta Isra’ila Tzipi Livni da ke jagorantar nata bangare domin shata muhimman batutuwa da za su tattauna a kai a birin Washington.

Bangarorin biyu dai sun katse tattaunawa ne tsawon shekaru uku saboda batun gine gine da Isra’ila ke yi a yankunan Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.