Isa ga babban shafi
Amurka

An ceto wasu ‘Yan mata 150 da ake fataucinsu a Amurka

Hukumar ‘Yan tsaro ta FBI a kasar Amurka ta ceto wasu matasa kimanin 150 da ake amfani da su wajen yin sana’ar karuwanci da kuma wasu da ke aikin kawalci, a kokarinta na kawar da fataucin yara a kasar.

Jami'an FBI da ke yaki da karuwanci a New Jersey, kasar Amurka
Jami'an FBI da ke yaki da karuwanci a New Jersey, kasar Amurka REUTERS/FBI/Handout via Reuters
Talla

Samamen da hukumar tsaron suka kai na tsawon kwanaki uku, an yi sa ne a cikin manyan biranen kasar guda 76, kuma samamen ya kasance na hadin gwiwar tsakanin jami’an tsaron da wasu kananan hukumomi da kungiyar da ke kula da yaran da suka bata da wadanda ake cin zarafin su a kasar mai suna NCMEC.

Matasan da aka ceto sun hada da masu shekaru 13 zuwa 16 a cewar mataimakin hukumar bincikien ta FBI Ronald Hosko.

Ya kara da cewar burinsu shi ne su ga an fito fili ana mahawara dangane da wannan lamari na fataucin yara kanana da ake yi domin sanya su karuwanci ko kuma cin zarafinsu a kasar, wanda ta hakan ne kawai za a iya fito da wannan matsalar fili.

Mista Ronald ya ce suna iya kokarinsu domin rage kaifin wannan matsala a Amurka, wadda ke faruwa kusan a boye a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.