Syria-MDD
Wakilan MDD za su isa kasar Siriya
Majalisar Dinkin Duniya tace, nan da ‘yan kwanaki ne wakilanta zasu shiga cikin kasar Syria domin tabbatar da zargin anfani da makamai masu guba, da aka haramta amfani da su a karkashin dokokin duniya. Majalisar ta Dinkin Duniya ta kuma ce Shuaban Syria Bashar al-Assad, ya amince ya ba wakilan damar shiga yankuna kasar guda uku da aka ruwaito an yi amfani da makamai masu guba a rikicin kasar da aka kwashe fiye da watanni 28 ana gwabzawa.Idan dai har aka gano ana amfani da makaman masu guba, Majalisar na iya bude kofar taimakawa ‘Yan tawaye, da makaman da za su yaki dakarun gwamnatin kasar.
Wallafawa ranar: