Isa ga babban shafi
Amurka

An yanke wa Manning hukuncin daurin shekaru 35

Wata Kotun Amurka ta yanke wa Sojan Amurka Bradley Manning hukuncin daurin shekaru 35 wanda ya mika dubban bayanan sirrin kasar ga Wikileaks da ke kwarmata bayanan sirri. Tuni aka kori Manning daga aikin soja saboda ya ci amanar kasa da laifin satar bayanan Amurka 700,000 da ya mika wa shafin Wikileaks.

Sojan Amurka Bradley Manning wanda ya mika dubban Bayanan sirrin Amurka ga Wikileaks
Sojan Amurka Bradley Manning wanda ya mika dubban Bayanan sirrin Amurka ga Wikileaks REUTERS/Gary Cameron
Talla

Da farko masu gabatar da kara sun nemi a yanke wa Manning hukuncin daurin shekaru 60.

Sojan na Amurka ya amsa laifinshi na mika bayanan sirri da suka kunshi yakin Amurka a Afghanistan da Iraqi tare da neman afuwa bayan ya hankalin kasar.

A shekarar 2010 ne aka cafke Manning a kasar Iraqi, kuma tun a lokacin ne ake ci gaba da tsare shi.

Sai dai kuma an wanke sojan daga laifin taimakawa makiya musamman al Qaeda, amma dubban mutane ne suka nemi a ba Manning kyautar Nobel ta zaman lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.