Isa ga babban shafi
EU-Syria

Kwamitin tsaro na EU na fatar gani an warware rikicin Syria ta hanyar sulhu

Shugaban kwamitin tsaro na Majalisar kungiyar kasashen Turai, Arnaud Danjean, yace babu wata ribar kirki da za’a samun wajen kaiwa kasar Syria hari sojin, inda yake cewa ta hanyar tattaunawa ce za’a iya magance rikicin kasar.

Arnaud Danjean Shugaban kwamitin  tsaro na Majalisar Kungiyar Nahiyar Turey
Arnaud Danjean Shugaban kwamitin tsaro na Majalisar Kungiyar Nahiyar Turey © Stephane Rabut/Wikipedia
Talla

Dan Majalisar wanda ya nuna shakku sa kan bayyanai da kasar Faransa ta ce tana da su kan hari da makami mai guba, yace har yanzu a koi shakku kan bangaren da yayi amfani da wanan makamin mai guba.
Dan Majalisar , ya ce Yan Tawaye na iya anfani da makamin dan dora laifin ga shugaba Bashar al Assad,
Inda ya kara da cewar a koi tambayoyin da dama dake bukatar amsa kafin sanin wanda yayi anfani da makamin.
Dan Majalisar ya nuna adawar sa kan yunkuri kaiwa Syria hari da kasashe keta ikirarin, domin idan aka kaiwa shugaba Assad hari na karamin lokacin, wata hanya ce ta bashi damar yi anfani da muggan makamai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.