Isa ga babban shafi
Syria

Yadda duniya, 'Yan tawaye ke kallon shirin karbe makaman Syria masu guba

Bisa ga dukkan alamu za a iya kaucewa yunkurin da kasar Amurka ke yi na kaiwa kasar Syria hari bayan shawarar da kasar Rasha ta bayar, na saka makamai masu guba na kasar ta Syria a karkashin kulawar kasashen duniya, lamarin da ‘yan tawayen Syria suka nuna rashin amincewarsu da shi inda suka ce dabara ce da gwamnatin Syria ta dauka domin ta jinkirta harin da za a kai mata.

Taron kasashe masu kawance da yria
Taron kasashe masu kawance da yria
Talla

Kungiyar kasashen Larabawa ce dai ta fara nuna amincewar ta da shawarar da Rasha ta bayar na saka makamai masu guban mallakar Syria a karkashin kular kasashen duniya, inda shugaban ta Nabil al – Arabi ya ce akwai bukatar a lalata makaman da zaran an samesu.

Itama Faransa wacce ta marawa yunkurin baya, ta amince da wannan tayi sai dai Ministan Harkokin wajen kasar, Laurent Fabius ya nuna akwai bukatar shugaba Bashar a Assad ya fito fili ya fadi yawan makamai masu guba da Syria ta mallaka.

Ana ta bangaren Amurka, wacce itace ke yunkurin jagorantar daukan matakin soji a kasar ta ce a shirye take ta jinkirta yin hakan, idan dai Syrian da gaske take tabi umurnin baje makamanta masu guba domin kasashen duniya su kula da su.

Ita kuwa kungiyar tarayyar Turai cewa ta yi maraba da wannan tayi sai dai za ta zira ido ta ga ko wannan yunkuri zai haifar da da mai ido, yayin da Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ke cewa akwai bukatar a lalata makaman idan har aka saka su a karkashin kular kasashen  duniya.

To sai dai yayin da shugabannin duniya ke nuna amincewarsu da wannan mataki, su kuwa ‘Yan tawayen Syria sun nuna rashin cikakkiyar amincewa da wannan mataki, suna masu cewa akwai bukatar kasashen duniya su duba sauran batutuwa baya ga batun makamai masu guba da kasar ta Syria ta mallaka.

Tuni dai gwamnatin ta Syria ta nuna amincewarta ga wannan shawara da Rasha ta bayar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.