Isa ga babban shafi
Kenya

An cafke wasu mutane da ake zargi na da hanu a harin Kenya

‘Yan sandan kasar Kenya sun sanar da cafke mutane sama da 10 wadanda ake zargi suna da hanu a wani hari da mayakan kungiyar Al Shabab suka kai a wani babban shagon kasuwanci dake Nairobi domin amsa tambayoyi game da harin.  

Lokacin da hayaki ke tashi a shagon kasuwanci na Wastegate inda ake arangama da 'yan kungiyar Al Shabab da dakarun kasar Kenya
Lokacin da hayaki ke tashi a shagon kasuwanci na Wastegate inda ake arangama da 'yan kungiyar Al Shabab da dakarun kasar Kenya REUTERS/Johnson Mugo
Talla

Cafke mutanen na zuwa ne a dai dai lokacin da bayanai daga kasar Kenya ke nuna cewa akalla mutane sama da 60 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu daruruwa suka jikkata.

“Mun cafke fiye da mutane 10 domin su amsa tambayoyi akan ahrin da aka kai a babban shagon kasuwancin Wastegate.” In ji ‘Yan sanda a wani sako da suka wallafa a shafin Twitter.

Mayakan na Al shabab a yanzu haka na yin garkuwa da mutane da dama a shagon yayin da dakarun kasar ta Kenya ta kai wani sabon farmaki akan maharan inda suka kashe mutane uku.

An kuma ji harbe harbe yayin kai wannan sabon hari yayin da aka ga hayaki na tashi bayan wata fashewa da ta biyo baya.

Tun dai a ranar Asabar aka fara wannan arangama da maharan na Al Shabab wadanda suka dauki alhakin kai harin a shagon kasuwancin wanda ya kasance wani wuri da 'yan kasashen waje ke zuwa yin cefane.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.