Isa ga babban shafi
Syria

Hukumar dake haramta yaduwar makamai masu guba za ta tura tawaga ta biyu zuwa Syria

Hukumar dake haramta yaduwar makamai masu guba a duniya ta ce za ta tura tawaga ta biyu ta kwararrun zuwa Syria domin cimma burinta na lalata makaman Syria. 

Tawagar motocin kwararrun MDD a Syria
Tawagar motocin kwararrun MDD a Syria REUTERS
Talla

Hukumar ta bayyana hakan ne a wata rubutacciyar sanarwa da ta fitar a yau Litinin ta na mai cewa hakan zai karawa tawagar farko karfi wajen gudanar da aikin.

“Haka zai taimaka wajen ganin mun tabbatar da cewa an lalata makaman.” Kamar yadda sanarwar ta fitar.

Tun makon da ya gabata ne tawagar farko ta isa
kasar inda ta fara gudanar da ayyukanta.

An dai ba hukumar wa’adin daga nan zuwa tsakiyar shekarar 2014 domin ta lalata makaman na Syria a karkashin wata amincewa da Majalisar Dinkin Duniya ta yi a watan da ya gabata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.