Isa ga babban shafi
Syria

Kasashen da ke goyon bayan 'yan tawayen Syria za su halarci taro a London

Ministocin Kasashen Larabawa da takwarorin sun a kasashen Yammacin duniya dake goyan bayan ‘yan Tawayen Syria, suna shirin halartar wani taro a London, dan rarrashin Yan Tawayen su halarci taron zaman lafiyar da ake shiryawa a Geneva. Su ‘yan Tawayen na bukatar ganin an cimma yarjejeniyar saukar shugaba Bashar al Assad daga karagar mulki, abinda bangaren shugaban ke cewa ba zai yiwu ba.Su dai kasashen Yammacin duniya sun ce babu yadda za’a warware rikicin Syria ta hanyar soji, dole sai an koma teburin tattaunawa. 

Shugaban kasar Syria, Bashar al-Assad
Shugaban kasar Syria, Bashar al-Assad Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.