Isa ga babban shafi
EU-Amurka

Shugabannin Turai za su gana a lokacin da suke takun saka da Amurka

Shugabanin kungiyar kasashen Turai za su fara gudanar da taronsu a Brussels a yau Alhamis, inda za su mayar da hankali kan batun tattalin arziki da kuma matsalar bakin hauren da ke mutuwa kan hanyarsu ta tsallakawa Turai. Taron na zuwa ne a dai dai lokacin da kasashen na Turai ke zargin Amurka tana sauraren zantukan mutane a wayoyin Salula.

Shugaban Amurka Barack Obama tare da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel
Shugaban Amurka Barack Obama tare da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel
Talla

Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta bukaci bayani daga shugaban kasar Amurka Barack Obama kan zargin sauraren zantukanta a wayar tarho.

Merkel ita ce shugaba ta baya bayan nan da ta nemi bayani daga Amurka, bayan shugabanin kasahsen Faransa da Mexico da Brazil.

Fadar shugaba Obama ta musanta zargin tare da ikirarin kaucewa aikata nadar bayanan shugabar.

Shugaban Faransa Francois Hollande ya nemi a saka batun sauraren zantukan Mutane ya kasance cikin batutuwan da shugabannin za su tattauna bayan fitar da wani rahoto wanda yace Amurka tana sauraren zantukan Miliyoyan Faransawa a wayoyinsu na Salula.

Akwai maganar mutuwar Bakin haure da shugabannin na Turai za su tattauna wadanda ke kokarin tsallakawa daga kasashen Afrika.

Gabanin Taron na kasashen Turai, kasar Faransa ta bayyana fargaba da damuwa akan bakin haure da ke mutuwa a cikin Tekun Mediterranean a lokacin da suke kokarin tsallakawa zuwa Turai.

Laurent Fabius babban Jami’in Diflomasiyar Faransa yace Talauci ne ke sa mutunen Afrika tsallakawa zuwa Turai ba don yawon bude ido ba, kuma ya yi kira ga sauran kasashen na Turai su lalabo matakan magance matsalar musamman tantance kan iyakokin kasashen da ke gabar Teku.

Akwai dai wani jirgin Ruwa shake da bakin haure da ya nutse wanda ya janyo hasarar rayukan mutane sama da 300.

Mista Fabius yace akwai kudiri da Faransa ke kokarin gabatarwa a zauren taron game da hanyoyi magance matsalar.

A jiya Laraba akwai wata ganawa da wasu Ministocin harakokin wajen kasashen Turai suka yi tare da takwarorinsu na kasashen Arewacin Afrika game da matsalar mutuwar bakin haure da ke neman tsallakawa zuwa Turai.

Amma Duk da matakan da kasashen Turai zasu dauka game da bakin haure, dole akwai bukatar sai kasashen Afrika sun dauki matakan magance kwararar mutanen Nahiyar zuwa Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.