Isa ga babban shafi
Syria-MDD

Brahimi yace dole a bar Iran ta halarci taron da za a yi kan kasar Siriya

Manzon MDD da kungiyar kasashen larabawa dangane da rikicin Syria Lakhdar Brahimi, ya ce dole ne a bai wa kasar Iran damar halartar tattauwar zaman lafiyar da kasashen duniya ke shirin gudanarwa a birnin Geneva cikin watan gobe, da nufin warware rikicin kasar ta Syria. Brahimi, wanda ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan ganawarsa da ministan harkokin wajen Iran Mohammad Jawad Zarif a birnin Tehran, ya ce ba ta yadda wannan taro zai samu nasara ba tare da halartar kasar ta Iran ba.Ita dai Iran na a matsayin daya daga cikin kasashen da ke goyon bayan shugaba Bashar Assad na Syria a daidai lokacin da wasu kasashen larabawa, Turai da kuma Amurka ke goyon bayan ‘yan adawan kasar.  

Mai shiga tsakani a rikicin kasar Siriya Lakhdar Brahimi
Mai shiga tsakani a rikicin kasar Siriya Lakhdar Brahimi United Nations/Mark Garten
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.