Iran-Syria
Rohani yace dole a kori ‘Yan ta’adda a Syria
Shugaban Kasar Iran, Hassan Rohani, ya shaidawa mai shiga tsakanin rikicin kasar Syria, Lakhdar Brahimi cewar dole ne a kori ‘Yan ta’adan da ke cikin Syria kafin a samu zaman lafiya. Rohani yace ci gaba da kai kayan agaji Syria da korar ‘Yan ta’adda a cikin kasar da kuma lalata makamai masu guba, shi ne matakin farko na samun zaman lafiya a kasar.
Wallafawa ranar:
Talla
Brahimi yace lallai Iran na da rawar da zata taka wajen warware rikicin kasar Syria a taron Geneva.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu