Isa ga babban shafi
Vietnam

Guguwar “Haiyan” ta doshi yankin Vietnam

Fiye da mutane 600,000 aka kwashe daga muhulansu a kasar Vietnam yayin da mahaukaciyar guguwar Haiyan ta doshi yankunan kasar. Hukumomin Vietnam sun ce sun yi hakan ne domin kaucewa lamarin day a faru a Philippines.

Guguwar Haiyan a lokacin da take barna a Philippines
Guguwar Haiyan a lokacin da take barna a Philippines REUTERS/ABS-CBN via Reuters TV
Talla

A karshen makon da ya gabata ne guguwar ta yi daidai da wasu yankunan kasar ta Philippines lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane ya kuma barnata wurare da dama.

Rahotannin sn guguwar wadda ke tafiyar kilomita 35 a cikin kowace sa’a yanzu haka ta doshi kasar ta Vietnam.

Guguwar wadda aka yi mata lakabi da “Haiyan’ na a matsayin wadda ta fi kowace muni da ta taba afka wa kasar, yayin da hukumomin kasar Australiya ke cewa akwai ‘yan asalin kasar da suka rasa rayukansu a guguwar wanda a halin yanzu ta doshi kasar Vietanam.

Rahotanni har ila yau na nuni da cewa an jingine tashi da saukar jirage guda 62 a kasar ta Vietnam.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.