Isa ga babban shafi
Faransa-Iran-Amurka

Hollande da Obama sun lallashi Iran akan Nukiliya

Shugaban Amurka Barack Obama da takwaransa na Faransa Francois Hollande, sun bukaci hukumomin kasar Iran da su amince da shawarwarin da kasashen duniya suka gabatar masu dangane da batun shirin Nukiliyar kasar.

Shugaban Amurka Barack Obama yana zantawa da Hassan Rohani, a fadar shi ta Washington.
Shugaban Amurka Barack Obama yana zantawa da Hassan Rohani, a fadar shi ta Washington. "AFP PHOTO / THE WHITE HOUSE / Pete SOUZA"
Talla

A wata sanarwa da aka fitar jim kadan bayan sun tattauna ta wayar tarho a yammacin Alhamis shugabannin biyu sun bayyana cikakken goyon bayansu dangane da matsayar da kasashen duniya suka cim ma dangane da batun nukiliyar kasar Iran a birnin Geneva cikin makon jiya.

Shugabannin sun kuma ce akwai bukatar samun tabbaci daga Iran, cewa shirin ba ya da wata nasaba da aikin soja, suna masu cewa ta hakan ne kawai kasashen duniya za su iya gamsuwa Iran ba ta da wata boyayyar manufa a wannan batu.

A cikin makon da ya gabata, Iran da kuma manyan kasashen duniya guda shida, sun kasa cim ma matsaya a tattaunawar kwanaki uku da suka gudanar a tsakaninsu a birnin Geneva, sai dai dukkanin bangarorin biyu sun yarda cewa an samu gagarumin ci gaba a lokacin tattaunawar.

A wannan karo dai hukumomin birnin Tehran sun zargin Faransa da taka muguwar rawar da ta sa aka tashi baram baram a wannan tattaunawar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.