Isa ga babban shafi
Brussels-Tsakiyar Afrika

Kasashen Turai suna nazari akan Afrika ta tsakiya a Brussels

A yau Alhamis kungiyar Tarayyar Turai za ta fara wani taron kwanaki biyu inda ake sa ran batun rikicin kasar Jamhuriyar Tsakiyar Afrika zai zamo babban batu a taron da za a yi a Birnin Brussels.

Ministan tsaron Faransa, Jean-Yves Le Drian, a lokacin da ya kai ziyara a garin  Bangui babban birnin Jamhuriyyar tsakiyar Afrika
Ministan tsaron Faransa, Jean-Yves Le Drian, a lokacin da ya kai ziyara a garin Bangui babban birnin Jamhuriyyar tsakiyar Afrika AFP PHOTO/FRED DUFOUR
Talla

Taron na zuwa ne kwanaki biyu bayan shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya nemi kasashen Turai da su kawo dauki a kokarin samar da zaman lafiya da Faransa ke jagoranta a kasar ta Jamhuriyar Tsakiyar Afrika

Ana sa ran Shugaba Francois Hollande zai yi wani jawabi a gaban taron, inda zai yi bayani game da lamarin da ake ciki a kasar Afrika ta Tsakiya.

A farkon makon nan Dakarun Faransa suka fara kwance damarar yakin kungiyoyin mayakan sa kai domin dawo da zaman lafiya a rikicin na addinin da ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane a makon da ya gabata.

Faransa a yanzu haka na da dakaru sama da dubu daya jibge a Bangui, babban birnin kasar tun bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da tura dakarun kasar da na Tarayyar Afrika.

Sai dai duk da kasancewar dakarun, rahotanni na nuna cewa hankula ba su gama kwantawa ba, lamarin da ya sa Faransa ta yi kiran sauran kasashen Turai da su kai mata dauki.

A yanzu haka kasar Belguim na duba yiwuwar aikawa da dakaru 150 yayin da Amurka ke jigila dakarun kasar Burundi zuwa Jamhuriyar tsakiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.