Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Salva Kiir ya yi watsi da sharadin da ‘yan tawayen kasar suka shimfida

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta yi watsi da sharadin da bangaren ‘yan adawa suka shimafida na asaki wasu daga cikin wadanda ake rike da su kamin su hau teburin tattaunawa. Wannan na zuwa ne yayin da shugaban Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki -moon ke ikrarin za a kara yawan dakarun dake wanzar da zaman lafiya a kasar.  

Shugaban kasar Sudan ta Kudu, Salva Kiir
Shugaban kasar Sudan ta Kudu, Salva Kiir RFI/Pierre René-Worms
Talla

Rahotanni daga kasar na cewa dukkanin bangarorin biyu na Shugaba Salva Kiir da na tsohon matiamakin shugaba Riak Machar na da burin a sasanta rikicin siyasar kasar ta hanyar tattaunawa.

Sai dai batun sakin wasu ‘yan adawan da ake tsare da su ga dukkan alamu zai maid a hanun agogo baya a yunkurin shawo kan rikicin.

Lamarin da ya sa Ministan yada labaran kasar Michael Makieu, ya ce babu yadda za su saki mutanen da ake zarginsu da yunkurin juyin mulki, yana watsi da ikrarin da ‘yan tawayen ke yi na cewa sun karbe muhimman filayen man kasar.

“Babu yadda za mu saki mutanen da ake zargi da yunkurin juyin mulki.” Inji Makieu.

Manzon kasar Amurka na musamman a kasar ta Sudan ta Kudu, Donald Booth ya gana da wasu daga cikin mutanen da ake tsare da su, kuma sun bayyana mai shirinsu na a kawo karshen rikicin cikin ruwan sanyi.

Tuni dai wakiliyar Amurka a majalisar Dinkin Duniya, Samantha Power ta yi gargadin cewa muddin bangarorin biyu basu sasanta ba, za a ci gaba kashe mutanen da ba su san hawa ba ba su san sauka ba.

Yanzu haka ‘yan gudun hijra sama da dubu 45 ne ke fake a ofishin Majalisar Dinkin Duniya yayin da wasu dubbai suka fantsama zuwa wasu wurare.

A yau Ban ya nemi da a kara yawan dakarun dake kasar ninki biyu domin dakile wutar rikicin dake ruruwa zuwa wasu sassan kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.