Isa ga babban shafi
Faransa-Iran-Amurka

EU zata fara cire takunkumin da ta sanya wa kasar Iran

A ranar Litinin mai zuwa Kungiyar Taraiyyar Turai ta EU, za ta fara cire Takunkumman da ta kakabawa kasar Iran, lura da cewar Iran ta fara aiwatar da yarjejeniyar da ta kulla da Manyan kasashe masu karfin fada a ji a Duniya da aka gudanar a Geneva.Ministocin kassahen Nahiyar Turai ne za su sanar da wannan mataki a birnin Brussels na kasar Belgium.Hukumar kula da makaman kare dangi ta Majalisar dunkin Duniya IAEA, ta tabbatar da hakan, inda ta cewa Iran ta fara aiwatar da yarjejeniyar da aka yi da ita a birnin Geneva.Wata majiya daga kungiyar tarayyar Turai ta bayyana cewar da sanyin Safiya ne ake sa Ran Hukumar ta IAEA zata amince da batun cire Takunkumman, a kuma aiwatar da batun a wannan Ranar ta Litinin.A karkashin wannan yarjejeniyar da aka gudanar a cikin Watan Nuwamba, hukumomin birnin Tehran zasu dakatar da aikin da ake yi, na sarrafa sinadarin uranium zuwa matakin da za a iya amfani da shi wajen sarrafa Makamai, na akalla kashi 5 har na tsawon Watanni 6 a kuma cire wa kasar kashi 20 daga cikin Takunkumman da aka kakaba mata a baya.Yarjejeniyar zata kuma kawo karsen tauyewa Iran Biliyoyin Kadarorin da take da su a Amurka, yayinda kungiyar tarayyar Turai zata cire Dokar hana safarar Danyen Man kasar, lamarin daya janyo raguwar akalla kashi 50 na yawan Man da Iran ke fitarwa.Haka kuma tarayyar Turai zata cire Dokar hana sayar da Zinarin kasar Iran da ma suaran nau’in Karafa, kazalika da wasu albarkatun karkashin kasa. 

Abbas Araghchi Wakilin Iran a zaman tattauna batun Nukiliya da kasashen Duniya
Abbas Araghchi Wakilin Iran a zaman tattauna batun Nukiliya da kasashen Duniya ISNA
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.