Isa ga babban shafi
Faransa-Amurka-Iran

Faransa ta mayar wa Amurka da Martani akan Iran

Gwamnatin Faransa ta mayar da martani kan sukar da Amurka ta yiwa tawagar ‘Yan kasuwar kasar da suka tafi kasar Iran, don kulla huldodin kasuwanci. Kasar Amurka ta yi barazanar karfafa wa kasar Iran takunkumi domin yin gargadi musamman ga wakilan kasashe irin su Faransa da suka kai ziyara Tehran domin kulla huldar kasuwanci.

Pierre Moscovici, Ministan Kudin Faransa
Pierre Moscovici, Ministan Kudin Faransa RFI
Talla

Kasar Amurka ta yi barazanar karfafa wa kasar Iran takunkumi domin yin gargadi musamman ga wakilan kasashe irin su Faransa da suka kai ziyara Tehran domin kulla huldar kasuwanci.

Ministan kudin Faransa ne Pierre Moscovici ya mayar da martanin, inda ya ke cewa ziyarar ba ta kasuwancin yanzu yanzu ba ne, sai dai kulla hulda don gaba.

Ministan yace, bai dace Amurka ta kalli ziyarar ‘Yan kasuwarsu a matsayin neman kulla kasuwanci ba, sai dai nazari kan abinda zai zo nan gaba.

A cewar Moscovici, idan Iran ta sauya hanyoyin huldarta da kasashen duniya, to nan gaba za’a samu habakar kasuwanci da kuma tattalin arzikin kasashen duniya.

Yanzu haka dai tawagar ‘Yan kasuwan Faransa 116 suka kai ziyara a Iran, matakin da ya harzuka Amurka, har ya sanya ta gargadi kasar.

Wadanda suka kai ziyara Tehran sun kunshi har da wakilan kamfanonin kasar Faransa irinsu Total da Peugeot, domin kulla kawancen kasuwanci da kasar.

Irin wannan ziyarar ce Firaminsitan Turkiya, Recep Tayyip Erdogan ya jagoranci tawagar ‘Yan kasuwar kasar zuwa Iran.

Wannan kuma bayan an sassutawa kasar Iran jerin takunkumin da kasahen Turai da Amurka suka kakkaba mata bayan cim ma yarjejeniya game da batun Nukiliya.

Mataimakin Shugaban kungiyar kwadago wanda yana cikin tawagar da suka kai ziyara yace sun je ne domin diba yadda kasuwarsu za ta karbu a kasar bayan janye takunkumin Turai.

Amma kasar Amurka ta kalubalanci ziyarar domin a cewar sakataren harakokin waje John Kerry har yanzu akwai takunkumin da ke kan wuyan Iran.

Amurka tace takunkumin da suka sassautawa Iran na wuccin gadi ne har sai yarjejeniyar da suka kulla akan dakatar da ayyukan kera Nukiliya ta nuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.