Isa ga babban shafi
Faransa

Kasafin kudi a fannin tsaro zai karu a Duniya-Bincike

A wani rahoton da aka fitar na wata cibiyar da ke bin didigin lamuran tsaro da makamai a duniya IHS ya yi hasashen cewa a karon farko tsawon shekaru biyar, kasafin kudin da ake warewa fannin tsaro zai karu a bana musamman a yankin Asia da Gabas ta tsakiya da kuma Rasha.

Wani harin Bom da Kungiyar Taliban ta kai wa Dakarun NATO a yankin Samangan, a kasar Afghanistan
Wani harin Bom da Kungiyar Taliban ta kai wa Dakarun NATO a yankin Samangan, a kasar Afghanistan Reuters / Stringer
Talla

Rahoton yace adadin kasafin kudin zai karu da sama da kashi daya bayan shafe shekaru adadin na raguwa musamman a kasashen Turai.

Daraktan cibiyar ta IHS yace a tsawon shekaru biyu da suka gabata an samu karuwar kasafin kudin tsaro a kasashen Rasha da China da India da Saudi Arebiya da Oman.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yace zai yi kari ga kasafin kudin da ake kashewa a Fannin tsaro inda tuni adadin da Rasha ke kashewa ya fi adadin da Birtaniya da Japan ke warewa fannin tsaro.

03:17

Bakonmu A yau: Dakta Bawa Abdullahi Wase masani Sha'anin tsaro

Salissou Hamissou

Kasar Amurka ce dai tafi sauran kasashen Duniya kashe kudi a fannin tsaro kuma adadin yanzu sai raguwa ya ke yi bayan kasar ta fice daga yaki a kasashen Afghanistan da Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.