Isa ga babban shafi
Syria-Amurka

Amurka za ta Takurawa Syria-inji Obama

Shugaban kasar Amirka Barack Obama yace zasu duba matakan kara takurawa Shugaban kasar Syria Bashar Assad, ganin yadda batun tattauna zaman lafiya a kasar ke neman faskara.Shugaba Obama na fadin haka ne yayin da yake karban bakuncin  Sarki Abdallah na biyu na kasar Jordan.Shugaba Obama yace Amirka zata dauki matakin da ya dace cikin gaggawa kuma Amurka za ta ci gaba da hada kai da masu ruwa da tsaki gameda lamarin kasar Syria domin a kaiga nasara.A wajen wannan ganawa Shugaba Barack Obama yayi alkawarin tsayawa don bada rance na kudi Dolan Amurka bilyan daya ga kasar ta Jordan bayaga sabunta zumunci na tsawon shekaru biyar. 

Shugaban kasar Amirka Barack Obama tare da Sarki Abdallah na Jordan yayin ziyarar ranar Juma'a
Shugaban kasar Amirka Barack Obama tare da Sarki Abdallah na Jordan yayin ziyarar ranar Juma'a rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.