Isa ga babban shafi
Ukraine-Amurka-Rasha

Amurka ta nemi Rasha ta gana da Ukraine

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya nemi ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov, ya yi tattaunawa ta gaba da gaba da takwaranshi na Ukraine, kan rikicin yankin Crimea.

Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Amurkan ta gargadi Rasha kan yiwuwar rasa kujerarta a kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki ta G8.

John Kerry, daya yi aiki kut da kut da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov kan rikicin kasar Syria, ya nemi bangarorin biyu su tattauna da juna.

Wannna na matsayin takun sakan daya fi kowanne zafafa tsakanin Rasha da sauran kasahsen yammacin duniya, tun bayan yakin cacar baki.

A wani bangaren kuma sakataren baitul malin kasar ta Amurka Jacob Lew, gargadi ya yi kan yiwuwar dakatar da Rasha daga kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya ta G8.

Ya ce ba zai yiwu ba Rasha ta ci gaba da taka irin rawar da take takawa a Ukraine, sannan a barta ta karbi bakuncin taron shugabnnin kungiyar ta G8, a watan Yuni.

A halin da ake ciki, manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Ukraine Robert Serry, ya katse ziyarar da yake yi a yankin, bayan wasu ‘yan bindiga, da ba a san ko su waye ba, sun mishi barazana da ranshi.

Tun farko sai da aka yi ta yada jita jitar sace Serry a yankin na Crimea.

To a halin da ake ciki, kungiyar tarayyar turai ta EU, ta bayar da sanarwar wani gagarumin tallafin kudi da ya kai a kalla Yuro Biliyon 11 da za ta baiwa kasar Ukarine cikin shekaru kadan masu zuwa.

Shugaban hukumar Tarayyar ta Turai, Jose Manuel Barroso da ya bayar da sanarwar tallafin, ya kuma bayyan kaduwa ta tashe tashen hankulan da suka dabaibaye yankin Crimea a kasar ta Ukraine.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.