Isa ga babban shafi
Philippines-Amurka

Ziyarar Obama a Philippines

Shugaban Kasar Amurka Barack Obama ya kai ziyara a kasar Philippines daga kasar Malaysia bayan jami'ansa sun sanya hannu akan yarjejeniyar tsaron da hukumomin Manila inda anan ne zai kammala ziyarar da ya ke yi a kasashen Asiya.

Barack Obama na amurka tare da  shugaban Philippines Benigno Aquino
Barack Obama na amurka tare da shugaban Philippines Benigno Aquino REUTERS/Francis R. Malasig
Talla

Shugaba Obama ya sauka a Manila ne sa'oi bayan sanya hannu kan yarjejeniyar tsaron da za ta bai wa Amurka damar kai dakarunta da kuma kayayyakin yaki cikin kasar.

Mutanen kasar Philippines na adawa da kasar China, wadda suke ganin a matsayin kasar da ke masu barazana a Yankin.

Sai dai ba duka 'Yan kasar Philippines ke murna da sanya hannu kan yarjejeniyar da Amurka ba, yayin da wasu suka yi ta zanga-zanga a kusa da fadar shugaban kasar, kafin sanya hannu kan yarjejeniyar.

Masu zanga-zangar na kallon wannan yarjejeniya a matsayin wani mulkin mallaka da Amurka ke shirin sake yi wa kasarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.