Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

Rasha ta mayarwa Amurka da Turai martani kan takunkumi

Kasar Rasha ta mayarwa Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai martani kan sabbin takunkuman da aka kakaba mata game da rikicin kasar Ukraine, inda ta bayyana matakin a matasayin wani abu da “babu hankali a ciki.”

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergie Lavrov
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergie Lavrov REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

Ministan hakokin wajen kasar ta Rasha Sergie Lavrov, yayin ganawa da takwaransa na Cuba, Bruno Rodriguez ya ce basu amince da dukkanin takunkuman ba.

“Ba mu amince da dukkanin takunkuman da aka saka mana ba, musamman ma takunkuman da kasar Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai suka saka.” Lavrov ya ce.

A jiya litinin, Amurka da kawayenta hade da Kungiyar ta Tarayyar Turai suka saka sabbin takunkuman kan kasar ta Rasha a ci gaba da tankiyar da ake yi a rikicin kasar Ukraine.

Rahotannin sun nuna cewa takunkuman za su fi mayar da hankali ne kan wasu mutanen kasar dake da tasiri kan tattalin arzikin kasar ta Rasha.

Sai dai game da batun rikicin na Ukraine, Lavrov cewa ya yi “muna da burin mu ga an sasanta rikicin da wuri.”

Ya kuma kara da cewa shirin sasantawar, dole sai ya kasance ya bawa kowa damar ya fadin albarkacin bakinsa muddin ana so a sasanta.

Dangantaka tsakanin Rasha da Amurka da kuma wasu kasashen duniya ya yi tsamari ne tun bayan da Rasha ta karbe yankin Ukraine makwanni kadan bayan da aka hambarar da tsohon shugaban kasar ta Ukraine Viktor Yanukovych mai ra’ayin kasar Rasha daga kan karagar mulki.

Al’amura sun kara dagulewa ne tun bayan da wasu ‘yan aware suka kunno kai a gabashin kasar ta Ukraine, inda suke nema a balle a koma karkashin Rashan, lamarin da ya haddasa rikici da asarar rayuka a yankin.

Kasar Amurka da sauren kasashe, suna zargin Rasha ne da ruruta wutar rikicin yankin gabashin na Ukraine, zargin da Rashan ta ke musanta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.