Malala: Mayakan Boko Haram sun jahilci Musulunci
Dalibar Makarantar Pakistan Malala Yousafzai, da ‘Yan Taliban suka harba tace ‘Yan mata sama da 200 da Mayakan Boko Haram suka sace a Najeriya tana ganinsu tamkar ‘Yan uwanta ne a tattaunawarta da Kafar CNN.
Wallafawa ranar:
Malala da ke gwagwarmayar tabbatar da ilimin Mata, tace Mayakan Boko Haram sun jahilci addinin Islama kuma wadanda ba su san ilimin Al Qaur’ani ba.
Malala tace a lokacin da ta ji labarin an sace Mata a Najeriya sai ta ji kamar ‘Yan uwanta ne ke rayuwa a gidan yari.
A shekarar 2012 ne Mayakan Taliban suka harbi Malala saboda gwagwarmayarta na tabbatar da ilimin ‘ya’ya mata a kasar Pakistan, inda yanzu haka kuma ta ke rayuwa a Birtaniya bayan ta samu sauki.
Akwai manyan kasashen duniya yanzu da suka yi alkwalin za su taimakawa Najeriya domin kubutar da Matan sama da 200 da aka sace a Chibok cikin Jahar Borno da ke arewa maso gabacin Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu