Isa ga babban shafi
Brazil 2014

Ana ci gaba samun zanga zanga a Brazil

‘Yan sanda a Brazil sun kama a kalla mutane 18, a lokacin da suke zanga zangar adawa da gasar cin kofin dunita da ake yi a kasar. ‘Yan sandan sun kuma yi amfani da barkonon tsohuwa, inda suka tarwatsa wasu magoya bayan kungiyar kwallon kafan kasar Argentina, da ke kokarin tayar da zaune tsaye a birnin Rio de Janeiro.Kafafen yada labarun kasar sun ce, ‘yan sandan sun kuma kama wasu mutane 15, dake dauke da makamai da suka hada da wukake, bam da ake hadawa da Fetur da abun fufe fuska, don samun kariya daga hayaki mai sa kwalla. 

Wasu masu zanga zanga a birnin Sao Paulo na Brazil
Wasu masu zanga zanga a birnin Sao Paulo na Brazil REUTERS
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.