Isa ga babban shafi
Iraqi-Amurka

Obama yana nazarin yadda zai taimaki Iraki

Shugaban Amurka Barack Obama yana nazarin yadda zai taimakawa kasar Iraki domin fatattakar Mayaka ‘Yan Sunni da suka karbe ikon wasu biranen arewacin kasar. Akwai alamun Amurka zata sake aikawa da dakarunta a kasar Iraki bayan janye dakarun a 2011.

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Wata majiya daga Fadar White House tace Obama zai yanke hukunci akan komawa yaki a Iraki da kansa ba tare da ya yi dogaro da amincewar Majalisa ba.

Tuni gwamnatin Iraki, ta nemi taimakon Amurka don kaddamar da hare haren jiragen sama kan Mayakan da suka kai hari kan bututun man kasar, tare da kame wasu yankunan kasar.

Sai dai kuma Amurka na dari-dari da bukatar Iraki.

Amma Ministan harkokin wajen kasar Hoshyr Zebari, yace karfin soji kadai ba zai magance wannan rikicin kasar ba a yanzu.

Yanzu haka rikicin Iraki ya shiga rana ta Tara yayin da bangarorin biyu ke ikrarin suna samun nasara a yunkurin da suke yi na karbe wasu yankuna kasar.

Bayanai dai na nuna cewa kasar Amurka ta kashe biliyoyin daloli wajen horas da dakarun Iraki cikin shekaru da dama, lamarin da ya sa ‘yan jam’iyar Republican ke kalubalantar gwamnati Shugaba Barack Obama.

Kodayake, duk da jajircewar da Amurkan ke yi, ta tura wasu jiragen yakinta na sama zuwa yankin Gulf da kuma Karin sojojin domin kare ofishin jakadancinta da ke Bagadaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.