Isa ga babban shafi
Saudi

Kungiyar Musulmi ta yi alkawalin hada kan Musulmi

Kungiyar Musulmi ta OIC da ke wakilatar al’ummar Musulmi sama da biliyan daya da rabi a duniya tace zata yi kokarin hada kan Musulmi wajen samar da sabbin tsare tsaren tafiyar da gwamnati da za a kaucewa nuna banbancin akida a kasashen Musulmi.

Ministan Harakokin wajen kasar Saudiya Saud al-Faisal
Ministan Harakokin wajen kasar Saudiya Saud al-Faisal bdlive.co.za
Talla

Kungiyar ta yi wannan alkawalin ne bayan kammala wani taron kwanaki biyu a birnin Jeddah na Saudi Arebiya.

Yanzu haka banbancin akida ne ke neman kassara kasar Iraqi inda gungun wasu Mayaka mabiya akidar Sunni suka karbe ikon wasu biranen arewacin kasar da nufin karya gwamnatin Shi’a.

Kodayake a cikin sanarwar Kungiyar, da ta fito daga ministan harakokin wajen Saudiya Yarima Saud al-Faisal ba a ambaci rikicin kasar Iraqi ba, amma an bayyana matsalar banbanci akida a kasashen musulmi da dama.

Yerima Faisal ya zargi Firaministan Iraqi Nuri al-Maliki a matsayin wanda ya haddasa rikicin kasar tare da nisanta Saudiya da rikicin akan tana taimakawa Mayakan Iraqi masu bin akidar Sunni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.