Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinawa

“ Kona matashin Bafalasdine aka yi da ransa”

Kafofin yada labarai a yankunan Falesdinawa sun ruwaito cewa matashin bafalasdine nan da aka kashe, kona shi aka yi da ransa, kamar yadda wani sakamakon binciken kisan matashin ya nuna. Matashin mai suna Mohammed Abu Khader an tsinci gawarsa ne a wani daji da ke gabacin birnin Kudus bayan an sace shi.

Suha, Mahaifiyar Mohammed Abu Khudair da aka kashe a birnin Kudus
Suha, Mahaifiyar Mohammed Abu Khudair da aka kashe a birnin Kudus REUTERS/Ammar Awad
Talla

Rahotanni da aka ruwaito sun ce wadanda suka gudanar da binciken sun ga hayaki na fita daga jikinsa wanda ke nuna kona shi aka yi.

Falasdinawa dai suna zargin Yahudawan Isra’ila ne suka kashe matashin domin daukar fansan kisan wasu matasa yahudawa guda uku da aka kashe.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.