Gaza: Masar tana karbar ‘Yan gudun hijira
Gwamnatin kasar Masar ta bude kan iyakar Rafah da ake shiga Gaza domin karbar Falasdinawan da suka jikkata a hare haren da Isra’ila ke kai wa a Zirin Gaza. Kamfanin Dillacin labaran Masar ya ruwaito cewa nan gaba likitoci zasu fara karbar Falasdinawa a wata asibiti da ke arewacin Sinai, kan iyaka tsakanin Gaza da Isra’ila.
Wallafawa ranar:
Amma Rafah nan ne mashigin da ake isa Gaza ba tare ketawa Isra’ila ba.
Kimanin mutane 70 aka ruwaito sun mutu tun lokacin da Isra’ila ta fara luguden wuta da jiragen sama a Zirin Gaza.
Likitoci sun ce yawancin wadanda suka mutu mata ne da yara kanana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu