Isra’ila da Hamas sun tsagaita wuta na sa’o’I 12
Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry da manyan Jami’an diflomasiyar Turai da na gabas ta tsakiya sun yi kira ga Isra’ila da Hamas su tsawaita wa’adin yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa’o’I goma sha biyu da suka amince kuma wadda ta fara aiki a yau Assabar.
Wallafawa ranar:
Isra’ila da Hamas dukkaninsu sun amince su tsagaita wuta ta tsawon sa’o’I goma sha biyu ga hare haren da suke kai wa juna a rikicin Gaza domin samun shigar da kayan jin kai ga Falasdinawa.
An shafe kwanaki 19 Isra’ila na kai wa Falasdinawa hari, kuma zuwa yanzu Kusan Falasdinawa 1,000 suka mutu a hare haren da Isra’ila a Gaza.
Jimillar Sojojin Isra’ila 37 ne suka mutu a rikici tsakaninsu da Mayakan Hamas na Falasdinawa.
Ministan harakokin wajen Faransa Laurent Fabius ya yi kira ga bangarorin biyu su tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa’o’I 12 da suka amince kamar yadda ya shadaiwa manema labarai bayan sun kammala tattaunawa da wakilan manyan kasashen duniya game da rikicin Gaza.
Isra’ila da Hamas dai sun amince su tsagaita wuta na wucci gadi saboda dalilai na jin kai, suna masu watsi da duk wani mataki na amincewa su tsagaita wuta mai dorewa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu