Isa ga babban shafi
Falesdinu-Isra'ila

Sakataren Majalisar dunkin Duniya yace za a gudanar da bincike kan harin da Izraela ta kai a kan wata makaranta a Gaza

Babban magatakarda na MDD Ban Kimoon ya bukaci a gudanar da bincike dangane da hare-haren da isra’ila ta kai wa wata makarantar MDD da ke yankin Gaza a watannin da suka gabata.

Le secrétaire général de l'ONU, Ban Ki-moon
Le secrétaire général de l'ONU, Ban Ki-moon REUTERS/Ammar Awad
Talla

Ban Kimoon ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a zirin Gaza, inda ya ziyarta bayan kammala taron kasashen duniya kan yadda za a tara kudade domin sake gina yankin da Hare haren Isra’ila suka lalata.

Goyon bayan da Ban Kimoon ya baiwa Faledinawa dai ya harzuka kasar Izraela wace ta yi kashedin cewa hakan zai iya gurgunta daukacin yinkurin da ake yi na samar da zaman lafiya tsakaninta da Faledinawan

A dai gefen kuma hukumomin tsaron Isra’ila sun ce daga yau laraba, duk wani bafalasdinen da shekarunsu ba su kai 50 ba, to ba za a ba shi damar shiga masallacin Kudus ba.

Hukumomin na Isra’ila sun ce, sun dauki wannan mataki ne, sakamakon tarzomar da wasu matasan Falasdinawa suka tayar a kusa da masallacin a makon da ya gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.