Isa ga babban shafi
Masar

Jami’ar Azhar ta la’anci ayyukan IS

Shugaban Jami’ar Al Azhar da ke birnin Alkhahira na Masar Sheikh Ahmed El Tayeb ya soki muradun kungiyar IS da ke da’awar Jihadi a kasashen Iraqi da Syria, da cewa muradunsu ya sabawa addinin Islama.

Taron yaki da Ta'addanci a Jami'ar al Azhar birnin Alkahira
Taron yaki da Ta'addanci a Jami'ar al Azhar birnin Alkahira REUTERS/Al Youm Al Saabi Newspaper
Talla

Shehin Malamin ya soki ayyukan kungiyar ne a lokacin bude taron duniya kan yaki da ta’addanci a birnin Al Kahira.

Yace wasu mutane sun Jahilci ma'anar Musulunci don haka ake danganta ayyukan IS da addinin.

Sheikh Tayeb yace matsaloli da suka shafi akida da siyasa da tattalin arziki suka haifar da mayaka irinsu IS da al Qaeda. Malamin kuma ya yi kira ga Amurka da kawayenta da ke yaki da IS su tunkari kasashen da ke taimakawa ta’addanci.

Wakilan kasashe da dama ne suka halarci taron wanda Jami’ar Al Azhar ta shirya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.