Isa ga babban shafi
Fadar Vatican

Duniya na gudanar da bukukuwan Kirismeti

Jagoran mabiya darikar Katotlika na duniya Paparoma Francis, wanda ke gabatar da jawabin ranar Krismeti daga dandalin St Peters, ya yi kakkausar suka a game da yawaitar tashe tashen hankula a sassa daban daban na duniya, tare da yin kira da a kawo karshen muzgunawar da ake yi wa tsirarun kiristoci musamman a Iraki da kuma Syria.

Paparoma na gaisawa da manyan fada-fada a fadar Vatican da ke St Peters
Paparoma na gaisawa da manyan fada-fada a fadar Vatican da ke St Peters Reuters/路透社
Talla

Francis wanda ke jagorantar addu’o’in kirismeti karo na biyu a tarihi, ya kuma bukaci a shiga tattaunawar da za ta iya samar da zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Palastinu, kamar dai yadda ya bukaci a kawo karshen rikicin da ke faruwa a kasar Ukraine.

Har ila yau jagoran na cocin katalika ya nuna damuwa a game da halin da ake ciki a wasu kasashen Afirka, musamman Najeriya da jamhuriyar Afirka ta tsakiya, sannan ya jajantawa al’ummomin kasashen Liberia, Sierra Leone da kuma Guinee Conakry da ke fama da cutar Ebola.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.