Isa ga babban shafi
Amurka-Kimiyya

An gano cire daskararren jin daga jikin masu ciwo zuciya yana jawo matsala

Wani Binciken kimiyya da masana kiwon lafiya suka gudanar, ya nuna cewar anfani da allura wajen cire gurbataccen jini ko kuma jinin da ya daskare a jikin mai fama da bugun zuciya, na iya haifar masa da cutar shanyewar jiki.Binciken da Jami’ar McMaster da Jami’ar Toronto suka jagoranta, shine irinsa ta mafi girma da aka gudanar a duniya, kuma an gabatar da rahotan ta ne a kwalejin dake kula da cutar zuciya dake San Diego a Amurka, kuma aka kuma wallafa a Mujallar kula da harkar lafiya da ake kira New England Journal of Medicine.Rahotan yace anyi gwajin ne akan mutane sama da 10,000 a kasashe 20, wanda ya nuna rashin ingancin anfani da allura wajen fidda jinin da ya daskare a jikin masu fama da ciwon zuciyar.Wadanda suka gabatar da rahoton sun hada da Farfesa Sanjit Jolly na Jami’ar McMaster da Michael G. DeGroot na Cibiyar horar da likitoci. 

Wasu motocin daukar marasa lafiya
Wasu motocin daukar marasa lafiya Reuters/路透社
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.