Isa ga babban shafi
Iran-Isra'ila

Isra’ila na adawa da yarjejeniyar Iran

Gwamnatin kasar Isra’ila ta yi kakkausar suka ga yarjejeniyar da manyan kasashen duniya suka amince da Iran game da dakatar da shirinta na mallakar makaman nukiliya. Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce amincewa da yarjejeniyar abu ne mai matukar hatsari ga zaman lafiyar duniya.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu REUTERS
Talla

A ranar Alhamis ne aka cim ma yarjejeniya tsakanin manyan kasashen duniya guda shida da Iran a kasar Switzerland bayan shafe shekaru 12 suna tattaunawa.

A yarjejeniyar, kasar Iran ta amince da dakatar da shirinta na mallakar makaman nukiliya, yayin da kuma manyan kasashen duniya Amurka da Faransa da Rasha da China da Birtaniya da Jamus suka amince su janye takunkumin da suka kakaba wa Iran.

Amma Isra’ila na ganin yarjejeniyar ba za ta zama dalilin dakatar da shirin Iran na mallakar makaman nukiliya ba.

A yau Juma’a Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya jagoranci wani babban taro tsakanin shi da manyan jami’an tsaron kasar domin tattauna matakan da kasar za ta dauka akan barazanar Iran.

Amma Faransa ta jaddadawa Iran cewa ya zama wajibi ta dakatar da shirinta na nukiliya idan har kasar na son a gaggauna cire mata takunkumi.

Ministan harakokin wajen Faransa Laurent Fabius ya ce har yanzu ba a cim ma yarjejeniya ba har sai sun tabbatar da Iran ta dakatar da shirinta na nukiliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.