Isa ga babban shafi
Amurka-Cuba

An gagara cimma matsaya a tattaunawar Amurka da Cuba

Wakilai daga kasashen Amurka da Cuba sun ce bangagrorin 2 sun gagara cimma yarjejeniya kan bude ofisoshin jakadancinsu, don dawo da huldodi tsaninsu, bayan da suka shafe shekaru suna wa juna kallon hadadrin kaji. Josefina Vidal da ta jagoranci tawaggar kasar Cuba a taron na birnin Washigton, tace dukkan bangarorin sun amince su ci gaba da tattaunawa cikin ‘yan makonni masu zuwa.Sai dai Vidal taki cewa uffan kan inda aka sami banbanci tsakanin kasashen, da suka dade suna yakin cacar baki, da kuma suke neman hanyoyin kawo karshen gabar rabin karni.Dama bangarorin sun shafe watanni suna tattaunawa, da nufin dawo da huldar jakadanci tsakaninsu. 

Shugaban kasar Cuba Raul Castro
Shugaban kasar Cuba Raul Castro Reuters/路透社
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.