Isa ga babban shafi
Amurka

An yanke hukuncin daurin rai da rai kan mai shafin Silk Road a Amurka

Wani alkalin kasar Amjurka ya yanke hukuncin daurin rai da rai kan mutumin da ya kirkiro wani shafin Internet, da ake amfani da shi wajen cinikin miyagun kwayoyi a sassan duniya. Zuwa yanzu an yi cinikin miyagun kwayoyin da kudin su ya kai Dala Miliyon 200 ta hanyar amfani da shafin, mai suna Silk Road.Wanna ne hukunci mafi tsanani, da za a iya yankewa Ross Ulbricht mai shekaru 31 a duniya, da aka samu da laifuka 7, da suka hada da cinikin miyagun kwayoyi, gudanar da kamfanin da ake aikata laifuka, satar bayanai ta Internet da halatta kudin haramun.Shafin Internet da Ulbricht ya kirkiro, ya kuma dauki kwangilar kashe mutane 5 kan kudi Dala dubu $650,000. 

Shugaban Amurka Barack Obama.
Shugaban Amurka Barack Obama. Reuters/路透社
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.