Isa ga babban shafi
Amurka

Jeb Bush ya kaddamar da takarar Shugaban kasa a Amurka

Tsohon Gwamnan jihar Florida Jeb Bush ya bayyana aniyarsa ta shiga takarar zaben shugaban kasar Amurka da za a gudanar a badi karkashin inuwar Jam’iyyar adawa ta Republican. Jeb wanda Dan gidan Bush ne, wato Da kuma Kani ga tsoffin shugabannin Amurka guda biyu ya shaidawa dimbin magoya bayansa tabbacinsa na iya lashe zaben kasar da za a gudanar a 2016.

Jeb Bush ya kaddamar da aniyar tsayawa takarar Shugaban kasa a Jami'ar Miami
Jeb Bush ya kaddamar da aniyar tsayawa takarar Shugaban kasa a Jami'ar Miami REUTERS/Joe Skipper
Talla

A lokacin da ya ke kaddamar da aniyarsa ta tsayawa takara, Jeb Bush ya shaidawa dimbin magoya bayansa a Jami’ar Miami cewa kasar Amurka na bukatar canji, da ci gaba bayan shafe shekaru 8 na shugabancin Barack Obama mai barin gado.

Jeb Bush ya caccaki gwamnatin Obama da mabiyansa Kerry da Clinton na rashin samarwa Amurka makoma mai kyau a diflomasiyar duniya

Bush ya ce zai karfafa danganta tsakanin Amurka da aminanta, kuma zai fara ne da Isra’ila
Ana ganin Bush zai zama babbar barazana ga Hillary Clinton da ke takara karkashin inuwar Jam’iyyar Democrat ta Shugaba Barack Obama.

Jeb Buch ya ce zai bi salon mulki irin na yayansa W Bush wajen farfado da tattalin arzikin Amurka.

Kuma ana ganin zai yi yakin neman zabensa da ayyukan ci gaba da ya gudanar a lokacin da yana gwamnan Jihar Florida.

Sai dai akwai ‘Yan takara da dama daga Bangaren Republican da ke hammaya da Bush wadanda suka hada da Senatoci guda hudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.