Isa ga babban shafi
Amurka-Al-Qaeda

An kashe shugaban Al-Qaeda Nasir al-Wuhayshi

Kungiyar Al Qaeda da ke kasar Yemen ta tabbatar da kashe mata shugaba Nasir al-Wuhayshi, wanda shine shugaba na biyu na kungiyar a duniya, sakamakon harin sama da sojojin Amurka suka kai kasar.

Shugaban Kungiyar al-Qaeda a yankin kasashen Larabawa Nasir al-Wuhayshi
Shugaban Kungiyar al-Qaeda a yankin kasashen Larabawa Nasir al-Wuhayshi AFP/Getty
Talla

A wata sanarwar bidiyo da ta fitar a shafin ta, Kungiyar ta ce harin ya yi sanadi mutuwar Wuhayshi ne da wasu Mujahidan Kungiyar biyu, kuma tuni ta nada Qassem al Rimi a matsayin magajin sa.

A wani labarin kuma kungiyar Ansar al-Sharia a Libya ta musanta kashe shugaban kungiyar Al-Mourabitoune, ta mayakan Jihadin kasar Algeria Mokhtar Belmokhtar kamar yadda ake ta ya yatawa.

Kungiyar ta ce harin na Amurka bai hallaka kowa ba.

Mokhtar Belmokhtar, tsohon shugaban kungiyar Aqmi da ke da alhakin kai mummunan harin ta’addanci kan mahakar isakar gas a kasar Algeria, ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama wanda akasarin su baki ne 'yan kasashen ketare.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.