Isa ga babban shafi
Syria-MDD

An lalata makamai masu guba ta Syria ta mika wa MDD

Hukumar yaki da bazuwar makamai masu guba a duniya ta ce a halin yanzu an lalata dukkanin irin wadannan makamai da kasar Syria ta mallaka kamar dai yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a yi. Hukumar wadda ke da babban ofishi a birnin Hague na kasar Netherlands, ta ce an loda dukkanin makamai masu guba da kasar ta Syria ta mallaka a kan wani jirgin ruwan sojin kasar Amurka mai suna Cape Ray kafin daga bisani a lalata su a wani wuri da ke tsakiyar teku.  

Tawaggar MDD, dake sa ido kan makamai masu guba a kasar Syria
Tawaggar MDD, dake sa ido kan makamai masu guba a kasar Syria REUTERS/Phil Nijhuis/Files
Talla

Hukumar ta ce yawan makaman ya kai ton dubu daya da 300, wadanda aka kwashe daga Syria, inda aka yi amfani da wani makamashi domin narkar da su a tsakiyar tekun.
A shekara ta 2013 ne dai kwamitin tsaro na Majalisar ta Dinkin Duniya ya bayar da umurnin kwace wa Syria irin wadannan makaman masu guba, bayan da aka yi zargin cewa sojojin shugaban kasa Bashar Assad, sun yi amfani da su a kan fararen hula a kusa da birinin Damascus.

A lokacin da wannan lamari ya faru, kasar Amurka ta yi barazanar yin amfani da karfin soja akan gwamnatin Shugaba Assad, abin da ake ganin cewa shi ne ya tilasta wa gwamnatin amincewa da mika wadannan makamai a hannun hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya, domin lalata su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.