Isa ga babban shafi

Rasha ta tsawaita takunkumi akan Turai

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bada umarnin tsawaita takunkuman hana saida wa kasashen Turai kayyakin cimaka daga kasar na tsawon watanni 12 nan gaba a matsayin mayar da martani ga takunkuman kariyar tattalin arzikin da kasashen na yammacin suka kakabawa kasarsa.

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin REUTERS/Alexander Nemenov/Pool
Talla

Wata sanarwa da fadar Kremlin ta shugaban Rasha ta fitar a jiya Laraba ta ambato shugaba Putin na cewa, ya dauki matakin tsawaita takunkuman hana tura kayyakin abincin ga kasashen Turai ne, na tsawon shekara guda a matsayin mayar da raddi kan tsawaita takunkuman kariyar tattalin arzikin da kasashen suka kakabawa kasarsa.

A ranar Talatar da ta gabata ne kungiyar Tarayyar Turai ta tsawaita takunkumanta kan kasar Rasha na watanni 6, har zuwa karshen watan Janairun 2016 dangane da abin da ta kira rawar da Rasha ke ci gaba da takawa a rikicin kasar Ukraine.

Takunkuman da suka shafi fannonin tattalin arzikin kasar ta Rasha da dama, sun haramta duk wata hada-hada da bankunan kasar, da sha'anin tsaro da kuma Man Fetur, a Nahiyar Turai nan da watanni 6 masu zuwa.

A watan Agustan 2014 ne dai, Rasha ta kakabawa kasahen Turai nata takunkuman na kin sayar masu da kayan abincin da take nomawa, bisa zummar suma su dandani radadin da suka dandanar da ita a takunkuman da suka sake kakaba ma ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.