Isa ga babban shafi
IRAN

Iran ta amince da wasu daga cikin bukatun yarjejeniyar Nukiliya

Yau talata ita ce ranar karshe domin cimma yarjejeniya tsakanin Iran da manyan kasashen duniya kan shirin nukiliyar kasar, to sai dai Amurka ta ce an cimma matsaya kan yadda masu bincike na Majalisar dinkin duniya za su rika kai ziyara a wasu muhimman wurare da aka zargin cewa Iran na gudanar da ayyukan nukiliya a cikinsu.

Sakataren wajen Amurka  John Kerry, da takwaransa na Iran Mohammad Javad Zarif da sauran kasashen dake tattauna shirin Nukiliyar Iran.
Sakataren wajen Amurka John Kerry, da takwaransa na Iran Mohammad Javad Zarif da sauran kasashen dake tattauna shirin Nukiliyar Iran. AFP PHOTO / POOL / SUSAN WALSH
Talla

Manyan Jami’an Amurka da ke halartar tattauwar da ake yi a birnin Vienna, sun ce Iran ta amince wakilan hukumar makamashin nukiliya ta duniya su rika kai ziyara hatta ma a wasu daga cikin barikokin sojan kasar, kuma ta ce tana goyon bayan haka domin kuwa ita ma kanta Amurka ba dukkanin barikokinta ne ta ke bari a ziyarta ba.

Bai wa Jam’ian Majalisar damar shiga barikokin soja da kuma wasu muhimman wurare da ake zargin cewa Iran na gudanar da shirinta na nukiliya a asirce, na a matsayin abinda ya hana samar da yarjejeniyar tsakanin bangarorin biyu, kuma matukar dai kasar ta amince da wannan mataki, to ko shakka babu kamar dai yadda manazarta ke cewa za a iya samun yarjejeniya a gaggauce.

Su dai manyan kasashen duniya na zargin iran da kokarin kera makaman nukiliya, yayin da kasar ke cewa shirin na ta na zaman lafiya ne, kuma sakamakon wannan takun-saka kasar Amurka, Tarayyar Turai da kuma Majalisar dinkin duniya sun sanya wa Iran takunkuman karya tattalin arziki daban daban.

Yanzu dai hankulan duniya sun karkata zuwa ga taron na birnin Vienna, wanda ya kamata ya kawo karshe a yau talata 30 ga watan yuni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.