Isa ga babban shafi
Amurka

Beyonce zata shiga bukin kalankuwar yaki da talauci a duniya

Shararriyar mawakiyar nan mai suna Beyonce zata halarci wani bukin kalankuwa kade kade, a birnin New York na kasar Amurka tare da Pearl Jam, da nufin isar da sakon yaki da talauci a duniya. Wannan ne karon farko da mawakiya Beyonce zata yi irin wannan wasan. 

Mawakiya Beyonce
Mawakiya Beyonce REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Cikin shekarar 2012 aka kaddamar da bukin kalankuwar, da ake yi duk shekara, wanda ke gudana tare da hadin kan MDD, inda masu sha’awar bada gudun mawar yaki da tsananin talauci ke samun damar halarta a kyauta.
Ranar 26 ga watan Satumba ake sa ran gudanar da wasan kade kaden wanna shekarar, da zai kunshi wasu Karin mawakan da suka hada da Coldplay, da marubucin waka kuma mawakin kasar Ingila Ed Sheeran, da dama ya sanar da shirin halartar wasan.
Beyonce tace bukin na wannan shekarar nada muhimmanci, ganin cewa dukkan mawakan zasu yi amfani da kwarewar da Allah ya basu wajen isar da sakon yaki da matsanancin talauci a fadin duniya.
Bukin kalankuwar, da a baya ake nuna shi a gidan talibijin din MSNBC na kasar Amurka kawai, zai sami damar isa sassan duniya a bana, ta dandalin YouTube a internet, dama sauran kafafen sadarwa masu yawa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.