Isa ga babban shafi
Colombia

‘Yan tawayen Colombia sun tsagaita wuta

‘Yan Tawayen FARC da ke kasar Colombia sun sanar da shirin tsagaita wuta na tsawon wata guda sakamakon bukatar hakan da kasashen duniya suka yi don kawo karshen tashin hankalin da aka kwashe shekaru ana yi tsakaninsu da dakarun Gwamnati.

‘Yan Tawayen FARC da ke kasar Colombia sun sanar da shirin tsagaita wuta na tsawon wata guda
‘Yan Tawayen FARC da ke kasar Colombia sun sanar da shirin tsagaita wuta na tsawon wata guda AFP PHOTO/ FARC-EP
Talla

Babban jami’in kungiyar da ke halartar taron sasanta rikicin a kasar cuba Ivan Marquez ya ce tsagaita wutar za ta fara aiki ne daga ranar 20 ga wannan watan na Yuli domin bude kofar yarjejeniyar tsagaita wuta da din-din-din

Shugaban kasar Juan Manuel Santos ya yaba da matakin amma kuma ya bukaci kungiyar ta kara azama don kawo karshen tashin hankali a Colombia.

Kasashen Cuba da Norway da Chile da Venezuela ke shiga tsakanin rikicin tsakanin ‘Yan tawayen FARC da gwamnatin Colombia.

Rikicin ‘Yan tawayen dai ya samo asali ne tun 1964, inda wasu sojojin kasar suka rikide suka koma ‘Yan tawaye, kuma an kiyasta sun kasha mutane sama da 220,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.