Isa ga babban shafi
Mexico

Shugaban 'Yan Kwaya ya sulale a gidan yarin Mexico

Shugaban Ma su safarar miyagun kwayoyin a kasar Mexico Joaquin Guzman da ake kira El Chapo ya sake gudu daga gidan yarin da ake tsare da shi a karo na biyu bayan ya tona rami a karkashin inda ake tsare da shi a cikin gidan yarin.

Chapo ya haka rame ne ya tsare a gidan Yarin da ake tsare da shi
Chapo ya haka rame ne ya tsare a gidan Yarin da ake tsare da shi REUTERS/PGR - Attorney General's Office
Talla

Tuni hukumomin kasar Mexico suka baza jami’an tsaro oan farautar El Chapo wanda ya tsere daga gidan yarin Altiplano da ke da nisan kilomita 90 daga birnin Mexico.

El Chapo na da yara da abokan hulda kan safarar hodar ibilis a fadin duniya, kuma an kama shi ne watanni 17 da suka gabata bayan ya kwashe shekaru 13 yana buya.

Kwamishinan tsaron Mexico Monte Alejandro Rubido ya ce an gano cewar El Chapo ya tsere ne lokacin da aka dai na ganin shi a na’urar da aka sanya a dakinsa, abin da ya sa aka shiga neman inda ya shiga.

Yan Sanda da sojoji 250 ke gadin gidan yarin inda ake tsare da shugaban masu safarar kwayun a Mexico.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.