Isa ga babban shafi
Malaysia

Za a binciki Jirgin Malaysia a Faransa

A gobe asabar, za a isar da wani bangaren jirgin da aka tsinta a tsibirin La Reunion dake Tekun India zuwa kasar Faransa domin gudanar da bincke akai . 

Bangaren Jirgin a hannun masu bincike
Bangaren Jirgin a hannun masu bincike REUTERS/Zinfos974/Prisca Bigot
Talla

Bangaren jirgin da ake kyautata zaton na jirgin Malaysia ne samfurin MH370 wanda ya yi batan dabo a bara za a fara isar da shi zuwa filin jiragen sama na birnin Parsi dake Faransa, inda daga nan za a mika shi ga masu bincike a birnin Toulouse domin fadada bincike akai wanda kuma zai taimaka matuka wajan bada bayanai kan yadda jirgin ya bace bayan ya debo mutane 239 a ranar 8 ga watan Maris din bara daga birnin Kuala Lampur na Kasar Malaysia, inda ya nufi birnin Beijing na China.

Suma dai hukumomin kasar Malaysia sun tabbatar a yau jumma’a cewa bangaren na jirgin ne lamarin da ya bada karfin gwiwar cewa da yiwuwar kwararrun na Faransa suma su bayyana cewa shi ne.

Tuni dai tawagar masu bincike na Malaysia suka isa birnin Paris domin jiran isowar wannan bangaren kamar yadda jogorar tawagar Abdul Aziz ya sanar.

Bacewrar jirgin dai wata babbar musiba ce da ta faru a tarihin sufurin jiragen sama a duniya .
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.