Isa ga babban shafi
Brazil

Ana zanga-zangar kin jinin Rousseff a Brazil

Dubun-dubatan Jama’a ne ke gudanar da bore a Brazil inda suka bukaci Shugaban kasar Dilma Rouseff ta yi murabus saboda mtasalar tattalin arziki da cin hanci da rashawa da ya yi wa kasar katutu.

Ana zanga-zangar kin jinin Dilma Rousseff a Brazil
Ana zanga-zangar kin jinin Dilma Rousseff a Brazil REUTERS/Paulo Whitaker
Talla

Masu zanga-zangar sun daura alhakin matsalar da kasar ke fama da shi na tattalin arziki kan Shugaba Dilma Rousseff da Jam’iyyarta, tare da kalubalantar shugabar kan matsalolin cin hanci da rashawa da ke gurgunta ci gaban kasar.

Dubban mutane ne suka yi jerin gwano a biranen Brasilia da Rio de Janeiro inda suke rera wake na adawa tare yin kira ga Rousseff ta yi murabus.

A karshen mako an gudanar da zanga-zangar ne cikin lumana ba tare da wani tashin hankali ba.

A cewar ‘yan sanda kasar akalla mutane dubu 137 ne suka yi jerin gwano, kuma akwai alamar adadin zai karu lura da yanayin da kasar ke ciki a yanzu musamman a Sao Paulo gari mafi girma da arziki a kasar, yayin da wadanda suka shirya ganganmi ke cewa mutane dubu 225 ne suka fito domin kyamar mulki Dilma Rousseff.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.