Isa ga babban shafi
IRAN-Birtaniya

Iran da Birtaniya za su bude ofishin jekadancinsu

Kasar Iran ta ce za ta sake buda ofishin jakadancinta da ke birnin London na Birtaniya a rana daya da Birtaniya za ta sake bude nata Ofishin da ke birnin Tehran.

Sakataren harakokin wajen Birtaniya Philip Hammond
Sakataren harakokin wajen Birtaniya Philip Hammond REUTERS/Ints Kalnins
Talla

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta ce za a bude ofisoshin jakadancin ne a ranar lahadi mai zuwa, a yayin wata ziyara da sakataren wajen Birtaniya Philip Hammond zai ziyarci Tehran.

Hammond dai zai kasance babban Jami’in diflomasiyar Birtaniya da ya fara kai ziyara a Tehran bayan shafe shekaru sama da 10.

A 2011 masu zanga-zangar kyamar kasashen yammaci sun kona ofishin jekadancin Birtaniya a Tehran, a lokacin ne kuma Birtaniya ta rufe ofishinta tare da korar jekadan Iran daga London.

Tun a ranar 14 ga watan Yuli manyan kasashen Turai ke aikawa wakilai zuwa Iran bayan cim ma yarjejeniyar nukiliya tsakanin kasar da Birtaniya da Faransa da China da Jamus da Rasha da kuma Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.