Isa ga babban shafi
Chile

Girgizar kasa ta kashe mutane a Chile

Wata girgizar kasa mai girman maki 8.3 data auku a Kasar Chile ta yi sanadiyar mutuwar mutane biyar tare da tilastawa dubban jama’a fice wa daga gidajensu.

Wasu daga cikin wadanda suka rasa gidajensu a lokacin da suke kokarin neman inda zasu fake
Wasu daga cikin wadanda suka rasa gidajensu a lokacin da suke kokarin neman inda zasu fake Fuente: Reuters.
Talla

Girgizar kasar wadda ta auku a ranar laraba a babban birnin Santiago, ta tilastawa kimanin mutane miliyan guda kauracewa gidajensu yayin da kuma ta haifar da ambaliyar ruwa a wadansu sassan Kasar, al-amarin da ake kallo a matsayin wani gardadi dangane da aukuwar ambaliyar ruwan na Tsumani.

Tuni dai shugabar Kasar Michelle Bachelet ta bayyana shirin ta na ziyartar sassan da girgizar kasar ta fi shafa wanda aka ce shine mafi munin ibtila’in da ya taba afka wa Kasar tun shekara ta 2010.

Wasu hotuna da aka watsa ta kafar talabijin sun nuna yadda jama’a suka yi cincirindo a kan titunan Kasar da kuma yadda ruwa ya cika manyan hanyoyi a wadansu birane musamman wadanda ke kusa da gabar ruwa.

Har ila yau girgizar Kasar ta jikkata mutane da dama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.